Amfanin Shan Shayin Gahawa Don Maganin Cutar Hanta |
Amfanin Shan Shayin Gahawa Don Maganin Cutar Hanta
Wani sabon binciken Birtaniya daga Jami'o'in Southampton da Edinburgh ya gano cewa shan gahawa na da nasaba da raguwar barazanar kamuwa da cutar hanta da ta tsananta.
Masu binciken sun gudanar da binciken ne kan kusan rabin miliyan na mutanen Birtaniya kuma sun gano cewa masu shan gahawa suna da kashi 26 cikin 100 na rage barazanar cutar hanta kuma kashi 49 cikin 100 na rage barazanar mutuwa sanadin cutar, idan aka kwatanta da mutanen da ba su shan gahawa.
Shan kofin gahawa sau uku zuwa huɗu a rana na da fa’ida sosai kamar yadda binciken ya nuna.
Da fatan al'umma dake fama da wannan ciwon na hanta za su mayar da hankali sosai wajen shan shayin gahawa domin magance ciwon na hanta. Wanda ba su da cutar ma suma suna iya yin amfani da gahawa domin yin rigakafi.