Amfanin Shan Ruwa Kafin Kwanciyar Jima'i Ga Miji Da Mata |
Amfanin Shan Ruwa Kafin Kwanciyar Jima'i Ga Miji Da Mata
Shan ruwa ana daf da soma Jima'i yana da matukar amfani ga miji da mata kafin Kwanciyar jima'i, inji masana.
Masanan sun jero wasu amfanin da duk wasu ma'aurata zasu iya samu muddin dai zasu sha ruwa kafin su yi Kwanciyar Jima'i. Ga abubuwan kamar haka;
1: Shan ruwa kamin kwanciyar Jima'i yana ƙarawa miji da mata ƙarfin jiki. Maimakon jin kasala ko nauyin jiki, kuna shan ruwa zaku samu kuzarin hawa gado.
2 Haka nan kuma shan ruwa kafin soma Jima'i yana tunkuɗo sha'awa. Koda kuwa daga cikin miji da mata sha'awar sa ko nata bai motso ba, shan ruwa zai iya motso da sha'awa.
3 Har ila yau shi shan ruwa ana daf da soma kwanciyar jima'i yakan taimakawa jini ya ƙara samun gudana a jikin ma'aurata yadda zai ƙara musu kuzari da lafiyar saduwa.
4 Shan ruwa kafin fara kwanci Jima'i yakan rage warin gumin jikin miji da mata a lokacin da suke tsaka da saduwa idan zufa ya keto musu.
Maimakon zufan jikinku ya riƙa fitowa da wari, idan kun sha ruwa hakan ba zai yiwu ba. Ko kuma zai ragu.
5 Zai taimakawa miji da mata yin fitsari bayan kammala Jima'i. Yanada kyau bayan Jima'i duk wasu ma'aurata su samu damar wanke mararsu ta hanyar fitsari. Hakan na iya taimaka musu wajen cire duk wani cuta da zai iya tsayawa a gabansu ko mafitsararsu. Don haka idan suka sha ruwa kamin Kwanciyar jima'i suna kammala Jima'i zasu tsaftace maransu.
Waɗannan sune daga cikin amfanin shan ruwa ana daf da fara kwanciyar jima'i tsakanin mata da miji. Sai dai kada ya zamanto cewa miji da mata sun sha ruwan da yawa yadda zai cika musu ciki ya kuma hanasu kataɓus. Ruwa dai za'a sha ɗan daidai ba sai an cika ciki ba.