Amfanin Ƴaƴan Tafasa Da Rai Ɗore |
Idan ana yin amfani da ganyen tafasa ko ƴaƴansa suna da tasiri sosai ga jikin dan adam da magance cutuka
Wani bincike ya gano cewa idan za'a yi amfani da ƴaƴan tafasa da rai ɗore a Nigeria, za'a iya maganin cututtukan dake damun al'umma a kasar.
Ganyen tafasa, saiwar tafasa da ƴaƴan tafasa dukkansu magani ne. Haka itama 'Rai Ɗore' saiwarsa, ganyensa duka maganine dake magance manyan cutuka dake wahalar da mutane a duniya.
Duk wanda ke son rage kitse a jikinsa ya nemi garin tafasa, a dafa ruwa kamar rabin kofi sai a zuba garin tafasa cokali biyu sai tace a sha. Idan ana shan wannan haɗin na tsawon sati biyu yana maganin hawan jini, yana rage kits.
Wanda ke fama da ciwon ulcer idan yana dafa garin tafasa yana sha zai samu sauki. Sannan duk mutumin dake fama da matsalar ciwon mantuwa da tunani idan ana shan garin tafasa za'a samu sauki.
Mutanen dake da matsalar rashin barci idan yana shan garin tafasa za'a dinga samun barci sosai. Masu fama da matsalar ciwo ko ƙaikayin ido idan suna shan ruwan tafasa za su samu waraka.
Ku latsa nan ku kalli video da cikakken bayani kan amfanin tafasa.