Alamomin Yadda Ake Gane Mace Aure Take So

Alamomin Yadda Ake Gane Mace Aure Take So
Alamomin Yadda Ake Gane Mace Aure Take So 

Masana Sun Bayyana jerin wasu Alamomin Yadda Ake Gane Mace Aure Take So 


Ko kunsan irin alamomin yadda ake gane mace ta isa aure, ko kuma yadda ake gane aure take so? Idan mace na son aure akwai wasu alamomi da take nunawa wanda idan aka gano hakan aure take so. Ga jerin alamomin kamar haka:


1. Idan kaga mace tana yini a cikin daki tana kwance bata fito ba aure take so


2. Idan kaga mace tana dadewa a cikin daki kuma idan ta fito sai aga tana bata rai idan an tambayeta mene ke damunta sai tace babu komai, aure take so


3. Idan kaga mace tana tsayawa da saurayi a kusa da inda babanta ko wani dan uwanta zai ganta bata jin Kunya, alamu ne dake nuna aure take so


4. Idan kaga mace tana furtawa saurayi kalmomin soyayya a gaban iyayenta bata jin kunya, aure take so


5. Idan kaga mace tana yawan ziyartar gidan kawayenta da sukayi aure tana manne musu, alamu ne dake nuna aure take so


6. Idan kaga yarinya tana yawan posting a facebook group ko a page ko a status dinta tana tsokanar maza, aure take so


7. Idan kaga yarinya tana yawan rungumar yara tana wasa dasu, aure take so


8. Idan kaga yarinya tana yawan wasa da maza tana sakar musu fuska, aure take so


Wannan wasu daga cikin alamomi na yadda ake gane 'yan mata aure suke so, da fatan Allah ka basu Mazaje masu son su da Kaunarsu bisa gaskiya da rikon amana. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post