Alamomin Sanƙarar Mama (Nono) Da Inda Mace Zata Duba Ko Tana Da Ciwon Da Kanta |
Alamomin Sanƙarar Mama (Nono) Da Inda Mace Zata Duba Ko Tana Da Ciwon Da Kanta
Idan mace tana da ciwon sankaran mama wato Breast Cancer, ga alamomin yadda za iya lura a jikin ta kamar haka:
(1) Zubar da jini daga kan nono. Wannan tana samun mata masu shekara 30 zuwa 40, ɓari ɗaya ko duka nonan.
(2) Zata lura da abu mai tauri cikin nono a masu ƙananan shekaru 15 zuwa 30.
(3) Girman nono zai ƙaru ya zama ƙato ya kai 20-30 cm. Akwai ciwo da kuma canjin launin fatar gun.
(4) Zata lura nonon na ƙullutu kuma tana laushi kuma tana kumbura mafi yawa tana farawa ne kwana kaɗan ya saura zuwa lokocin Alada.
Yadda Mace Zata Duba Kanta A Gida Ko Tana Da Ciwon (SELF BREAST EXAMINATION)
Wannan yana magana ne yadda mace za ta gano tana da matsalon nono kafin ta fara jawo matsala, sannan da samun nasara wajen magani.
(1) Amfani da ƴan yatsunki kinabin kowane waje a kan nono a hankali, haka za'ayiwa duka nonon biyu ko wacce karshen wata, idan da canji sai a garzaya zuwa asibiti.
(2) Ki tsaya a gaban mudubi ki ɗaga hannayenki sama ko bisa ƙugunki. Daga nan ki duba sosai domin duba banbanci tsakanin nonon ki guda biyu. Shima idan akwai matsalar a garzaya zuwa asibiti.
(3) Idan kin kwanta sai ki kwantar da kafaɗarki guda ɗaya kan filo, ki ɗaga hannun kafaɗar zuwa ƙeyarki, sannan kisa ɗayan hannun danbin ko ina a hankali akan nononki domin gano ko akwai canji.
Zamu kammala wannan topic da yanda mace zata kare kanta daga wannan ciwon da kuma yanda masu shi zasu lura da kansu kar ciwon ta kai su kasa.
Inabuqarar soyayyar zallah ga number ta 08138794604
ReplyDelete07018040725
DeleteDhcgjdc
ReplyDelete