Alamomin Da Mace Za Ta Gane Tanada Ciki (Juna Biyu)

Alamomin Da Mace Za Ta Gane Tanada Ciki (Juna Biyu)
Alamomin Da Mace Za Ta Gane Tanada Ciki (Juna Biyu) 


Alamomin Da Mace Za Ta Gane Tanada Ciki (Juna Biyu) 
 

Daga zarar ciki ya shiga mace za tasamu wasu alamomi da ba ta saba ji ba, (ma'ana alamomin juna biyu kenan). Daga cikin wadannan alamomin akwai wadannan kamar haka:

 

1- Ketare wata (daukewar jinin al’ada na wata)

2- Tashin zuciya

3- Gajiya

4- Amai

5- Nonuwa suna kara girma.

6- Zazzabin safe

7- Yawan fitsari

8- Yawan kwadayi


Sai dai, waɗannan alamomin ba za su tabbatar da cewa mace tana ɗauke da juna biyu ba, don haka abin da ya kamata ta yi a daidai wannan lokocin shi ne ta yi gwajin fitsari ko jini domin tabbatar da cikin.


An raba ciki zuwa zango uku:

1- Zango na farko yana farawa daga shigar ciki zuwa watanni uku.

2- Zango na 2 yana farawa daga watanni uku zuwa sati 6.

3- Zango na uku yana farawa daga watanni 6 zuwa haihuwa.


Hanyoyin da mace mai ciki za ta bi domin domin zama cikin ƙoshin lafiya

1- Idan mace ta yi ciki, yaron da yake cikinta yana zuƙar jininta saboda shi ne abincinsa. Wannan dalilin ya sa mata masu ciki suna yawan samun ƙarancin jini.


Yakamata ta samu nau’in abinci mai ɗauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan marmari:


  • Wake
  • Kifi
  • Nama
  • Kwai da sauransu


Da kuma ganye da kayan itatuwa kamar su


  • Salat
  • Kabeji
  • Alayyafo
  • Zogole
  • Lemu
  • Kankana
  • Apple (Tuffa) da sauransu.

 

Wanda cin abinci lafiyayya yana ƙarawa mata jini, lafiya, yana ƙarawa yaron da yake ciki lafiya da kaifin basira.


2- Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane.


a- Mace mai juna biyu bai kamata ta dinga aikin wahala sosai ba, ya kamata ta dinga hutu ko wacce rana.

b- Idan mace mai ciki ba ta da lafiya dole ta je asibiti domin gudun ka da ta yi amfani da maganin da zai zama mata matsala, ko zai ya kawo matsala ga yaron cikinta .

c- Tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna biyu domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka.

d- Macen da take yawan amai ya kamata ta yi amfani da busheshshen abinci wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya.


3- Zuwa awo (Antenatal) yana da amfani sosai wanda a lokocin awo za a auna a ga yadda yaro ya kwanta a ciki.


Kuma ana aunawa a ga wasu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su, kamar su:

1- Hawan jini

2- Ciwon sugar na masu juna biyu

3- Cutar kanjamau

4- Yawan Jini

5- Zazzabin cizon sauro

6 – Halamar Eclampsia


4- Muna gargadin mata da su dinga amfani da maganin karin jinin da ake basu a wajen awo (Antenatal).


Mafi yawan mata idan an basu maganin karin jini maimakon su yi amfani da shi kullum, ba sa yi, da sunan wai ba su son warin maganin, wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zai sa a hana mutum shan wannan maganin.


A sani dama can magani ba don dadi ake sha ba, illa dan neman lafiya da neman kariya daga rashin lafiya.


5- Sai Kuma daukan allurar tetanus, wannan wata allura ce da ake yi wa mata lokocin awon ciki, amma mafi yawa mata ba sa son wannan allurar saboda rashin sanin amfaninta.


Gaskiya wannan allurar tana da amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shi ne kare yaro daga kamuwa da wannan cutan mai hatsarin gaske wato (tetanus) .


6- Motsa jiki lokocin juna biyu na da amfani sosai, ga kadan daga ciki:


  • Yana taimako wajen rage ciwon baya, tashin zuciya, kumburin kafa da kuma kunburin Jiki.
  • Yana taimakawa wajen kare ko lura da ciwon suga na lokacin goyon ciki
  • Yana tamakawa wajen karin karfi jikin mace mai ciki 
  • Yana taimakawa wajen bunkasa yanayin jikin mace mai juna biyu 
  • Yana taimakon karfin jiki, jinya da kuma lafiyar jikin mai ciki 
  • Yana taimakon mai ciki wajen yin barci mai dadi


Abubuwan da yakamata mace mai ciki ta sani lokacin motsa jiki.

Ana so mace mai juna biyu ta saka kayan da suke matse jiki kamar rigar mama, da kuma ɗaure ciki dan kar a ji ba dadi

Ta kiyaye tsayuwa guri ɗaya a lokacin motsa jikin dan kar jini ya taru a kafa.

Ta kiyaye kwanciya a gadon baya, domin ciki yana tare da jijiyoyin na jini zuwa zuciya, hakan yana rage zuwan abinci ga yaron da ke cikin ciki.

Kada mace ta motsa jiki idan tana da waɗannan matsalolin kamar haka:


  • Ciwon zuciya:
  • Matsalar zubda ciki:
  • Rashin lafiyar mahaifa:
  • Nakuda kafin lokacin haihuwa:


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post