Alamomin ciwon sanyin maza |
Yadda ake gane lamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu a bainar mutane (game gari)
Akwai wasu alamomi na kamuwa da ciwon sanyi da maza ke dauka. Wannan sanyin gama gari ne domin ana samun maza da yawa suna yin sa.
1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.
2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).
3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko ɗorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
4. Jin zafi wajen yin fitsari.
5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.
6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.
Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba
1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
2. Zafi da kumburin maraina
3. Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
4. Zazzaɓi
Idan kuna bibiyarmu za mu dinga kawo muku hanyoyi da za ku yi maganin ciwon sanyi cikin sauki.