Abubuwan Dake Saka Mata Tumbi - Android Pols

Abubuwan Dake Saka Mata Tumbi - Android Pols
Abubuwan Dake Saka Mata Tumbi 


Kafin ki kwanta barci kada kici kowanne irin abinci, anason sa'o'i biyu bayan cin abinci sannan ayi bacci


Akwai yanayin abinci da ruwan shan, haka zalika akwai yanayin mu'amala na yau da kullum dake saka mata su zama masu tumbi wannan zahiri ne domin binciken masana tuntuni ya tabatar da hakan wanda ko a darusan baya mun kawo makaman tansu amma ayanzu zamuyi karin bayani dangane da wannan matsalar wanda kuma shawarwari ne ga mace idan tabi insha allahu ba ita ba zama me tumbi. 

Kafin ki kwanta barci kada kici kowanne irin abinci, anason sa'o'i biyu bayan cin abinci sannan ayi bacci, musamman abu me dumi ana so a baiwa jiki dama wannan abincin ya narke aciki kafin bacci, a takaice yawan cin abinci kafin bacci yana sakawa mace ta zama me tumbi. 

Cin abu me sanyi bayan tashi daga barci, anaso mace kafin taci komai ta sha abu me dumi, ba'aso asha abu me sanyi kamar lemo da yake da gas sosai a jikinsa, abari sai bayan an dumama ciki da abu me dumi. 

Yawan zama waje daya, anaso mace ta zama me yawan motsa jiki musamman matan aure anaso lokacin saduwa da miji mace ta zama me yawan motsa jikinta saboda anan jikinta yana mikewa yayi daidai, amma mace ta kwanta komai miji zaiyi yana saka jikin mace ya sake da wuri ta rinka yin tumbi. 

Yawan cin Abu me maiko musamman mata masu yawan zama waje daya yana kawo musu basir me kumbura ciki mace ta zama me tumbi kuma wanda bashida laushi, ga yawan tusa. 

Domin rabuwa da tumbi kuma akwai bayanin da yawa ku duba rumbum video da topics dinmu na Youtube da blog akwai wani wanda ake dafa lemon tsami bayan an yanyankashi sai a tace ruwan a saka zuma ana sha sau biyu a rana kafin a kwanta barci da kuma bayan an kwanta.

Wannan kuma za'a samu danyar kurkum da danyar citta a feresu duka sai a yanyankasu a zuba a ruwa shima lemon tsami a yanka guda daya sai asamu kanunfari kadan da tafarnuwa, sai a dafa wannan ruwan, ana so a zuba ruwan yanda zaiyi kwana uku anasha shikenan bayan ya tafasa sai a tace a saka zuma anasha sau biyu a rana har zuwa kwana uku.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post