Abubuwan Da Namiji Yake So Daga Wajen Matarsa A Rayuwar Aure |
Abubuwan Da Namiji Yake So Daga Wajen Matarsa A Rayuwar Aure
Ita dai mu’amala wata aba ce da ake so mutum ya kyautata ta, tsakanin sa da kowa, har wanda ba musulmi ba. Ya kamata mata su lura da wadannan halayen a zamantakewar aure, ga su kamar haka:
1) Biyayya
Dole ne a matsayin ki na matar aure ki kasance mai biyayya a cikin duk abin da mijin ki ya ce kiyi, idan har bai sabawa abin da Allah yake so ba. Ki ji a ran ki ke fa bautar Allah kika zo yi gidan aure, kuma ki sa a ranki cewa aure hanya ce da zaki nemi Aljanna da ita.
2) Gaskiya:
Fadin gaskiya a kowanne lokaci a zaman aure yana da muhimmanci kuma zai jawo miki kauna da soyayyar mai gidan ki. Haka kuma zai jawo miki yardar Allah. Manzon Allah (SAW) ya ce: “lallai ita gaskiya tana shiryar wa zuwa ga biyayya ga Allah, ita kuma biyayyar Allah tana shiryar wa zuwa Aljanna. Ita kuma karya tana shiryarwa zuwa fajirci, shi kuma farirci yana shiryar wa zuwa wuta.
Ashe dai fadin gaskiya zai iya jawo yardar Allah, domin kuwa in har an shiga Aljannah ai babu sauran fushin Allah kuma; kamar yadda karya zata iya jawo fushin Allah.
3) Rikon amana:
Ki kasance mai rikon amanar mijin ki. Ki kiyaye kan ki daga duk wani namiji wanda zai iya sa mijin ki na aure ya zarge ki a kan sa. Ki yanke alaka da duk wanda mijin ki baya son kiyi alaka da shi, kuma kar ki kulla wata alaka da duk wanda mijin ki baya so kiyi alaka da shi.
Ki kula da dukiyar sa, abin da ya shafi kayan amfani na gida ko kadarar sa ko kuma kudin sa. Ina jin labarin ana cewa wasu mata har duba aljihun mazajen su suke yi ko zasu samu kudi su dauka, 'yar uwa ta kar ki yi haka domin rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Kunya
Dole ne mace ta kasance mai kunya. Dole ne duk abin da zai sa mijin ta ya ji kunya a gaban jama’a ta kiyaye shi.
4) Hakuri
'Yar uwa ta kada kiyi tunanin rabin ran ki ba zai bata miki rai ba. Wasu matan idon su yana rufewa, wai don ita kadai ce ‘ya mace a gidan su ko ita ce ‘yar auta ko ita kadai aka haifa a gidan su, don haka yanda ake shagwaba ta a gidan su haka za’a yi mata a gidan mijinta na aure.
Hakan zai iya faruwa, in kin yi sa’ar mijin da yake da fahimta. Zaki iya samun wanda zai baki gatan ma da ya fi wanda kika samu a gidan ku, amma fa ki sa a ranki wata rana dole a samu matsala. To duk lokacin da matsalar nan ta faru kiyi hakuri ki manta da zancen. Wannan shi zai kara miki zaman lfy a gidan mijinki.