Abubuwan Da Namiji Yake Bukata Daga Wajen Mace - Android Pols

Mansura Isah: Abubuwan Da Namiji Yake Bukata Daga Wajen Mace
Abubuwan Da Namiji Yake Bukata Daga Wajen Mace


Abubuwan Da Namiji Yake Bukata Daga Wajen Mace 


Duk mace da ta tsaya ta Karanta wannan topic din zai yi matukar taimaka mata wajen tabbatar da soyayya da zaman lafiya tsakanin ta da mijinta ko mai son ta.

Ita dai mu’amala wata aba ce da ake so mutum ya kyautata ta, tsakanin sa da kowa ,har wanda ba yan addini 1 ba. Ya kamata mata su lura da wadannan halayen:

Gaskiya: Fadin gaskiya a kowane lokaci yana da muhimmanci kuma zai jawo miki kauna da soyayyar wajen masoyin ki. Domin ita gaskiya tana shiryar wa zuwa ga biyayya ga Allah, ita kuma biyayyar Allah tana shiryar wa zuwa Aljanna. Ashe dai fadin gaskiya zai iya jawo yardar Allah, domin kuwa in har an shiga Aljannah ai babu sauran fushin Allah kuma; kamar yadda karya zata iya dawo fushin Allah.

Biyayya: Dole ne a matsayin ki na mace ki kasance mai biyayya a cikin duk abin da masoyin ki ya ce kiyi, in har bai sabawa abin da Allah yake so ba. Ki ji a ran ki ke fa zaki iya yin komai don kauna. 

Rikon amana: Ki kasance mai rikon amanar masoyin ki. Ki kiyaye kan ki daga duk wani namiji wanda zai iya sa mai Sonki ya zarge ki a kan sa. Ki yanke alaka da duk wanda mijin ki baya son kiyi alaka da shi, kuma kar ki kulla wata alaka da duk wanda mijin ki baya so kiyi alaka da shi. Ki kula da dukiyar sa, abin da ya shafi kayan amfani na gida ko kadarar sa ko kuma kudin sa. Dole ne mace ta kasance mai kunya. Dole ne duk abin da zai sa masoyi ya ji kunya a gaban jama’a ta kiyaye shi.  


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post