Abubuwa Biyar dake fitar da Soyayyan Namiji daga Zuciyan Mace

Abubuwa Biyar dake fitar da Soyayyan Namiji daga Zuciyan Mace
Abubuwa Biyar dake fitar da Soyayyan Namiji daga Zuciyan Mace


Abubuwa Biyar dake fitar da Soyayyan Namiji daga Zuciyan Mace Cikin Kankanin Lokaci  


Soyayya gamon jini inji Hausawa, Akwai matukar dadi da annashuwa idan soyayya ta kasance tsakanin masoya har karshen rayuwa, kauna da kulawa dake zama a zukatan masoya ba game gari bace kuma ba abar dauka da wasa bace.


Soyayya na bukatan kulawa, raino lokaci da kuma abubuwa da yawa da ke iya sa ta dade na tsawon lokaci.


A wannan rubutun, zamu tattauna akan abubuwan dake sa soyayyar namiji ya fita daga zuciyan mace kwata-kwata, ga kadan daga cikin su;


(1) Rashin kula

Yawan lokacin da ka ba kanka wajen hira ko kuma kallon bal matan ka baka bata wannan lokacin balle ka fuskanci matsalan ta itama ta gane naka matsala, soyayya na bukatar kulawa tsakanin masoya.


(2) Yiwa mace rikon sakainar-kashi:

Wasu mazan na soyayya da mace amma kiran muntoci kalilan na gagaran su. Wannan nuna halin ko inkula din nasa mace ta daina jin soyayyar namiji kwata-kwata a ranta.


(3) Kalu-balanta akai-akai:

Mata basu kaunar namiji mai yawan kalu balantan su, kalu balanta na fara shiga tsakanin masoya ake samun babban matsala tsakanin ta da masoyin ta.


(4) Rashin biyan bukata:

Yawancin mata suna son suga namiji yana nuna musu yana son abinda suke so ko ba gaskiya bane, idan suna da bukatan abu ya nuna musu shima yana son wannan abu sama da su ma amma kuma ga yanayin da ake ciki sai Allah ya kawo.


(5) Nuna kauna:

Mata da yawa basu son namiji yana boye irin soyayya da yake musu  sunfi son a koda yaushe ya nuna kalan son da yake musu.


Wannan sune wasu daga cikin abubuwan dake jawo fitar soyayyar namiji daga zuciyar mace, domin su mata suna son a nuna musu soyayya kuma a nuna an damu dasu sosai. Da fatan maza za su dinga nuna kulawa sosai kan masoyansu. 


Daga Hajiya Mariya Azare

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post