Abubuwa 6 Da Zaka Yiwa Mace Idan Kana Sonta Da Gaske: |
Abubuwa 6 Da Zaka Yiwa Mace Idan Kana Sonta Da Gaske:
Duk namijin da zai daure ya yiwa macen da yake so da gaske wadannan abubuwan zai yiwa zuciyarta katutu yadda babu wani namijin da zai yi tasiri a ranta harma taji tana son sa. Kuna iya kallon wannan VIDEO don jin cikakken bayani Ga abubuwan kamar haka;
1: Ka nuna mata soyayyar ka a aikace ba da baka ba.
2: Kada ka takura mata wajen sakamata idanuwa ko neman mata bincike a rayuwarsa. Ka barta ta sakata ta wala ba tare da ka nuna mata kai namiji mai yawan zargi ko takura ba. Ku kalli wannan VIDEO.
3: Ka bata lokacinka. Kada ka zama sai ta nemeka take ganinka.
Ka zamanto namiji mai yawan kusantar ta a duk lokacin da ka fahimci ya dace ko take bukatar ganinka.
4: Ka girmamata. Kayi kokarin samun wani suna na musamman da zaka rika kiranta dashi domin girmamata.
Ya kasance kana yi mata magana cikin natsuwa da girmamawa amma ba da gadara ko isa ba. Haka nan ka kuma girmama na kusa da ita.
5: Matsalarta matsalarka ne. Kada ka barta tana fama ita kadai a lokacin da take cikin wani damuwa.
Ka kasance a tare da ita wajen nuna mata damuwarka akan duk wani abu na rashin jin dadi daya sameta. Kayi kuma iya kokarinka akan yadda zaka shawo kan lamarin.
Wannan kulawar ma'aunine da ake iya auna ko namiji zai iya kula da matarsa a lokacin daya aureta.
6: Ka Kiyaye yiwa wasu matan kwarkwasa ko magana a gabanta. Ka tabbatar da ka mutunta a duk lokacin da kake tare da ita da bayan ka rabu da ita wajen amsa ko Kiran wasu matan a waya. Ko kuma yawan kalle-kallen mata kana tare da ita.
Nasan wasu za su ce ba ayi zancen kudi ba. Gaskiya ne mata suna son kudi, amma sunfi son a nuna musu kulawa, a basu lokaci, ayi alfahari dasu a gaban duniya fiye da kudi.
Mace idan tana sonka kuma tanada yadda zata yi bazata kula kudin hannun wanda take so ba. Mata sunfi matsawa namijin da basason sa da gaske da bani bani. Shi wanda suke so sai dai su masa inkiya idan mai fahimta ne ya gano hakan.