Abubuwa 6 Da Mata Za Su Kiyaye A Rayuwar Auren Su - Android Pols

Maryam Yahaya: Abubuwa 6 Da Mata Za Su Kiyaye A Rayuwar Auren Su
Abubuwa 6 Da Mata Za Su Kiyaye A Rayuwar Auren Su 


Muhimman Abubuwa 6 Da Mata Za Su Kiyaye A Zamantakewar Rayuwar Auren Su 


1) Abu na farko da ya kamata ki sani kuma ki kiyaye shine daraja mijinki da kuma ganin girmansa da kimarsa, anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar auratayya. Kar wai dan kina ganin ya zama kamar abokinki ki rainashi, a'a anfi so mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban a cikin zuciyarta da kuma filin. 

2) Na biyu kuma shine ki girmama iyayensa da yan uwansa tamkar yanda zaki girmama naki iyayen da yan uwan ki. Kada ki kuskura kiyi aiki da wannan karin maganar wacce hausawa ke cewa "'ba a iya musu ya dangin miji"', duk namiji yana son a girmama iyayensa da yan uwansa.

3) Abu na uku shine ki zama mai matukar hakuri da juriya a gidan aurenki, domin zaman aure zama ne na hakuri da kawaici, ki k'i ji ki k'i gani sai ki zauna lafiya da mijinki. 

4) Abu na hudu kuma shine kar ki zama daya daga cikin matan nan masu bayyanar da sirrin mazajensu da sirrin gidan aurensu ga kawaye ko kuma abokan gaisawa, yin hakan haramun ne. 

5) Sai abu na biyar shine ki kasance mai tattalin dukiyar mijinki, ma'ana banda almubazzaranci da kayan miji, ki kasance mai tattalin dukiyarsa da kayansa domin kowanne namiji yana k'in jinin yaga yasha wahala ya nemo abu sannan an wulakanta. 

6) Abu na shida shine kar ki zama mai yawan bin k'wakk'wafin mijinki, komai yake yi idonki da kunnenki akai, kar ki zama haka domin maza basu kaunar mace mai bin diddigin abubuwan da suke yi. 

Wannan sune muhimman abubuwa 6 Da mata za su kula dasu a zamantakewar aure. Zaman aure dole sai an yi hakuri da kuma sanin abubuwan da za su tabbatar da dorewar auren.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post