Abubuwa 10 Da Namiji Ke Yi Wa Mace Idan Yana Son Ta Dagaske Da Aure |
Idan namiji yana son mace da aure, zai yi mata wadannan abubuwan 10
Akwai wasu abubuwa wanda idan namiji yana son mace zai dinga yi mata su da zai tabbatar mata dagaske yake sonta kuma so irin na aure ba na yaudara ba. Ga jerin abubuwan kamar haka;
1. Farkon abinda yake so wanda bai da burin da ya wuce yaga ya aure ta, domin auran ta yake son yi da gaskiyar sa.
2. Duk son da yake mata idan tayi kuskure bazai fasa gaya mata gaskiya ba,wannan shine soyayyar gaskiya, saboda idan kana son mutum koda zaiyi kuskure zaka gaya masa gaskiya,amma bawai mutum yyi kuskure kaki fada masa gaskiya ba.
3. Akwai son kyautata daidai karfin sa. Duk namijin da zai dinga yiwa mace kyauta ba tare da ta nema ba, yana nuna alamun zai aure ta.
4. Kulawa da tausayin ta, daidai iyawar sa zai na kulawa da ita yadda ba zai takura mata ba.
5. Akwai son iyayen ta da yan uwan ta don namiji idan son gaske yake yiwa mace yakan dauki iyayen ta nasa, hakama dangin ta komai duk abinda ya shafe ta zai zama yana girmama abin nan.
6. Ba zai taba neman wani abu daga gare ta ba wanda yasan bai dace ba.
7. Ko zance wanda babu amfani irin kazamar soyayyar nan bazaiyi da ita ba, saboda shi don Allah yake son ta kuma don ya aure ta.
8. Kokarin sa a kullum ganin yadda zata tsira da mutuncin ta a ko ina ma.
9. Zai gaya mata gaskiyar sa ba zai gaya mata abinda yasan cewa baya dashi ba.
10.duk wani matsalar ta zaina kokarin ganin ya mata maganin wannan matsalar nata koda ace bata hanyar kudi ba, zaiyi kokarin yi mata addu'a.
Wadannan sune muhimman abubuwa 10 da namiji ke yiwa mace su idan har yana sonta dagaske kuma da niyyar aure. Da fatan mata za ku kula da mai kaunarku dagaske ba masu yaudarar ku ba.