Ɗabi'u Da Ƴan Mata Ke Yi Wanda Ke Jawo Su Yi Shekaru Da Yawa Basu Yi Aure Ba |
Ɗabi'u Da Ƴan Mata Ke Yi Wanda Ke Jawo Su Yi Shekaru Da Yawa Basu Yi Aure Ba
Wasu matan ba rashin mazan da za su auresu bane ya hana su yin auren ba sai irin ɗabi'unsu ne ke haifar musu da matsala. Wasu matan sune matsalar kansu da kansu da suke koran mazan dake son auren su da kansu saboda wasu halaye da ɗabi'un su marasa kyau.
Hakan yasa muka tattaro muku wasu daga cikin dabi'u da ƴan mata ke aikatawa dake jawo su yi shekaru ba tare da aure ba. Ga jerin ɗabi'u nan wanda idan baki daina yin su ba. Haka zaki tsufa har ki rasa samun mijin aure.
1: Ruwan Ido:
Babban abinda ake jawo budurwa ta tsufa ba ta yi aure ba shine ruwan ido. Akwai matan da suke da ruwan Ido wajen zaɓen mijin da zasu aura. Duk wanda yazo su ajiye shi a gefe suna ƙoƙarin tara maza domin tantance guda a cikinsu ta hanyoyin da ba na Allah ba na son rai.
Duk namijin da ya zo neman auren budurwa da gaske, yaga kina raina masa hankali da ja masa rai, zai yi tafiyarsa ya rabu dake ya nemi wata daban. Daga bisani zaki daina ganin kowa na zuwa wajenki.
2: Alfahari Da Ji da Kai:
Akwai matan da su ba kowa ba, ba 'ya'yan wasu ba, amma alfahari da girman kai yasa basu da mu'amala mai kyau da mutane. Hakan har yake shafar mazan da suka zo aurensu. Hatta matan da suke da matsayi ko iyayensu muddin kina da alfahari da nuna isa hakan zai hanaki samun mijin aure da wuri har ki tsufa babu auren.
3: Saurin Fushi:
Duk macen da take da saurin fushi ko mafaɗaciya za ta jima bata samu mijin aure ba. Maza suna bukatar macen da take da haƙuri da sauƙin kai, saboda shi zaman aure sai da haƙuri. Amma da zaran maza sun gano baki haƙuri da sauƙin kai, sannan kina da saurin fushi ga fada ga rashin hakuri. Zaki dade a zaune a gidanku ki tsufa ba ki yi aure ba.
4: Ƙazanta:
Namiji ko da ƙazami ne so yake yaga ya auri mace mai tsafta da Iya ado da kwalliya domin burin za ta gyarashi ta kuma kula da abunda zasu haifa. Sai dai rashin tsafta na jiki da na tufa ga mace yana yi mata illar da maza basu zuwa neman auren ta.
5: Tara Maza:
Duk wata mace mai tara maza da sunan farin jini, daga ƙarshe za ta rasa mutum guda da zai ce zai aureta. Maza suna da fahimtar cewa, duk wata macen da take tara maza, tana iya kasancewa mazinaciya ce. Don haka masu sonta da aure za su kauce su bar masu nemanta da zina. Hakan zai jawo mata tsufa babu miji.
6: Tsananta Roƙon Kuɗi:
Ɗorawa namiji wani nauyi akai-akai da kuma yawan tambayarsa kuɗi dabi'a ce da kan iya hana budurwa samun mijin aure har ta tsufa.
Namiji ko mai kuɗi ne yana son ganin macen da zai aura mai sauƙin sha'ani ce. Da zaran ya fahimci ke macece mai son a baki kuɗi, zai rabu dake.
Abdunda akasarin mata suka kasa fahimta shine. Namijin da zai aureki ba zai so yayi ta yi miki hidimar kuɗi ba. Saboda gudun mai zai faru bayan aurenku. Amma shi namiji mai son yin lalata dake, bai damu da abunda zai kashe miki ba saboda aalaƙar taku na ɗan lokaci ne.
Waɗannan sune ɗabi'u da halaye da ƴan mata ke yi dake jawo wa budurwa ta yi tsawon shekaru ba tare da aure ba, ƴan mata da yawa suna rasa mijin aure har su tsufa a gida a dalilin waɗannan halaye da muka lissafa. Da fatan mata zasu farga su binciki dabi'un su domin ganin sun gyara.