Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida jikokinsa ('ya'ya na kenan) ya cigaba da kula dasu - Abdul Sahir

Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida jikokinsa ('ya'ya na kenan) ya cigaba da kula dasu - Abdul Sahir
Abdul Sahir

Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida jikokinsa ('ya'ya na kenan) ya cigaba da kula dasu - Abdul Sahir 

Jarumi a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdul Sahir wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shiri mai dogon zango na kwana casa'in, ya ce an dakatar dashi daga masana'antar ba bisa ƙa'ida ba, saboda haka ne yayi kira ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, akan cewa zai kawo masa jikokinsa domin ya cigaba da kula dasu. 

Cikin wani fefen bidiyo da ya wallafa a ranar Talata, Abdul Sahir (Malam Ali) ya bayyana gwamnan Kano a matsayin Uba a gare shi, don haka yake so ya miƙa masa 'ya'yansa kasancewar an dakatar dashi daga sana'ar da yake kula dasu. 

A ranar Litinin ne hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta dakatar Abdul Sahir tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da wallafa bidiyon da yake furta kalaman batsa, kuma ya ƙi amsa gayyatar da akayi masa domin kare kansa. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post