Ta Mutu Tana Saduwa Da Saurayinta Da Ya Sha Maganin Karfin Maza |
Yadda saurayi ya sha maganin karfin maza har ya wuce gona da iri ya kashe budurwarsa suna Jima'i
Wani saurayi ya sha maganin karfin maza da ya wuce gona da iri don ya nuna bajintarsa ga budurwarsa sai dai an yi rashin sa'a har yai sanadin mutuwarta.
Lamarin dai ya faru ne a jihar Kwara a wani hotel a yankin Temidire a Ilorin, babban birnin Jihar kamar yadda shafin Aminiya ya rawaito.
Bayanai sun nuna Isaac, wanda yake da shagon yin aski dai ya sha maganin ne da nufin birge budurwar tasa.
Wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Lokacin da suke saduwar, matar ta yi korafin cewa ta gaji, sannan jini na fitowa daga gabanta.
“Ana cikin haka ne aka ga ta daina motsi, inda aka garzaya da ita asibiti, kuma ta mutu a can.”
Bayan faruwar lamarin, saurayin ya jawo hankalin ma’aikatan otal din domin su kai masa ɗauki.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce, “mun kama saurayin sannan mun fara bincike domin gano ainihin abin da ya faru tsakanin shi da ita.”