Yadda Ake Yin Danwake Cikin Sauki

Yadda Ake Yin Danwake
Yadda Ake Yin Danwake


Yadda Ake Yin Danwake 


Yau a wannan rubutun za mu yi muku bayani a kan yadda ake yin dan wake. Shi dai danwake abincin gargajiya ne wanda kabilar Hausawa suke yinsa da sauran wasu kabilu kamar su Kanuri, Nufawa da sauransu. 


Da farko dai Idan za'a yi danwake ana bukatar wadannan abubuwa kamar haka


1 Kara ko itace sirara 

2 Ɓawon masara

3 Garin Danwake hadi na ainihi na ƙashin 

4 Rogo, wake, da jar dawa. 

5 Jiƙaƙƙiyar kanwa

6 Kukar miya.


Yadda Ake Hada Dan Wake 

Zaki samu ainihin garin Danwaken ki, ki tankaɗe sai ki kwaɓa kamar yadda zaki yi kwaɓin Danwake ki haɗa da ruwan kanwar, sai ki dauko ɓawon masarar da kika tanade shi falle-falle, ki bude tsakiya kina dibar kwaɓin kina mannawa a cikin ɓawon yayi tsayi ba gajeru ba. 


Bayan ruwan ki ya tafasa sai ki zuba kararen a cikin tukunyar ki yadda zasu kare ruwan kada ya zagwanyar da kwaɓin ki. Sai ki jera danwaken a kan cikin tukunya, sai ki rufe tukunyar ki na mintuna. Idan ya dafu zaki ji kamshi kuma ɓawon masarar zai canza launi baya daukar lokaci a kan wuta. Sai ki sauke ki zuba a ruwan sanyi, daganan sai ki cire ɓawon masarar. 


Zaki iya ci da kowanne irin mai da yaji ko miyar taushe,  Danwake yana da dadi da kosarwa. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post