Yadda Ake Hadin Karin Ni'ima Da Ayaba Da Gyada Mai Gishiri |
Wannan hadin Domin Ma'aurata ne kawai, Yadda Ake Hadin Karin Ni'ima Da Ayaba Da Gyada
Shin ko kunsan yadda ake yin hadin Karin Ni'ima idan aka hada ayaba, gyada mai gishiri da madara? Wannan dai wani nau'in sabon hadi ne da idan ma'aurata suka rike shi za su samu Karin jindadi a zamantakewar aurensu, ku kalli video.
Wannan hadin yana taimakawa ma'aurata su ji dadin gamsar da junansu a lokacin da suke yin Jima'i, sannan kuma hadin yana taimakawa wajen Karin ruwan maniyyi ga maza.
Ga Yadda Ake Yin Hadin
Ku samu wadannan abubuwan guda uku kamar haka;
1) Ayaba
2) Gyada Mai Gishiri
3) Madara ta sachet
Idan kun samu wadannan abubuwa uku da muka lissafa, za ku bushe bawon gyada sannan ku zuba a blander, ku bare bawon ayaba ku zuba cikin blander ku zuba madara ku markada su duka kamar yadda za ku ku gani a cikin wannan bidiyon. Idan kun so za ku iya ajiyewa cikin Firinji yai sanyi sannan ku sha.
Duk matsalar rashin sha'awa ko rashin samun gamsuwa a yayin Jima'i, wannan hadin na gyada da ayaba zai taimaka wajen inganta lafiyar jikin ma'aurata da kuma son yin Jima'i. Da fatan dai wanda ba su da aure ba za su yi amfani da wannan hadin ba.
Ku latsa nan ku kalli video cikakken bidiyon yadda ake yin wannan hadin.