Yadda ake Cin Amarya A Daren Farko

Yadda ake Cin Amarya A Daren Farko
Yadda ake Cin Amarya A Daren Farko 

 

Yadda ake Cin Amarya A Daren Farko 


Yaya Ake cin amarya a daren farko? Daren farko ko daren angwanci wani dare da ake farin ciki dashi musamman ga Sabbin ma'aurata, idan an wayi gari cikin sa rana ce masoya basa mantata a matsayin ranar farin ciki.


A wannan daren na farko ma'aurata suna  kasancewa a wani hali mai tattare da shauki da zumudi na kasance warsu a matsayin abu daya. Daren daraja ga ma’aurata kenan da zarar an kai amarya gidan mijinta ango kenan, Iyayanta da kawayenta zasu barta a daki tana jimamin kasancewar ta a wannan yana yi na zama amarya. 



Matakan Cin Amarya A Daren Farko

1) A ranar daren farko akan so bayan an watse ambar amarya ta tashi ta dan gyara abin da take ganin bazai kayatar mata da ango ba. A wasu gidajen ma'aurata kawayan amarya suna tsayawa har sai an kawo ango wannan baya cikin al’ada an fison abar amarya daga ita sai ango su ci amarci, shi kuma ango ya shigo ku yi abinda addini ya yarda dashi na sanar da ita yaya addini yake, idan kuma ta sani shikenan sai kuyi sallah ku yi godiya ga Allah ku ci daga abinda Allah ya baku a wannan dare domin more amarci. 


2) Na biyu shine kokarin tafiyar da Kunya a tsakanin ma’aurata, kasancewa sababbin ma’aurata duk baki suke ga wannan harka ta ibadar aure, dolene ya kasance akwai kunya da yar fargaba game da daren, don samun cikakkiyar nasara a daren farko, sai ma’aurata sun rage jin kunyar dake tsakaninsu, ya kasance suna tattaunawa kan batun ibadar aure, da yadda suke fatan daren farkonsu ya kasance. 


3) Yin dokin yadda ango zai ci amarya a daren farko ba shi ya kamata yasa a ransa ba, abinda ya kamata ango yai shine ya dasa kyawawan tunani cikin zuciya. A yayin kwanciya da amarya dole ne ango ne ya rika bi a hankali, cikin wasa da raha da zolaya ta hanyar amfani da kalmomi masu tayar da sha'awa ba masu nauyi ba, kuma ya kasance suna cike da shauki, har yaga ya zakulo amaryarsa ta rage jin kunya, idan ma dai ba ta daina ba, fada matan zai sa ta zama cikin sanin abinda ka iya faruwa. 


Haka kuma yana da kyau ma’aurata su nema tare da karanta littafai dake yi  bayani kan ilimin ibadar aure don a fahimce su. Domin da yawan amare suna shiga fargaba a ranar su ta farko da mijin da suka aura domin suna jin labarin irin yadda ake jin zafi da shan wuya idan za'a ci amarya a ranar farko. 


4) Shirya Jiki Da Jini, domin dai jiki da jini kamar inji ne ga fetur din gabatar da ibadar aure. Don haka yana da amfani ga ma’aurata su inganta lafiyar jikinsu da ta jininsu ta hanyar cin abinci mai kyau da gyara jiki musamman kayan ganyayyaki da ya’yan itatuwa da yawan motsa jiki da sauransu.


Wadannan sune matakan yadda ango zai ci amaryarsa a daren su na farko a matsayin ma'aurata. Da fatan kun gamsu kuma kun amfana daga wannan matakan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post