Al'ajabi
Labaran Ban Al'ajabi
Wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka
Thursday, November 9, 2023
0
Yadda wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka |
Wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa an harbe wani mutum a jihar wajen gwajin maganin bindiga daga wani Boka wanda ake zargin shi ne ya bai wa mutumin maganin bindigar sannan kuma ya harbe shi, tare da wasu mutane biyu yayin da sauran waÉ—anda ake zargi suka gudu.
Kakakin rundunar Æ´an sandan jihar, Ahmed Wakil ya bayyana cewa sunan wanda aka harba shi ne Muhammadu Ali, mai shekara 43, wanda aka kai shi Asibiti, sai dai an tabbatar da mutuwar sa a lokacin da suka isa.
Wakil yace za'a a gurfanar da waÉ—anda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike, ya kuma gargadi jama’a da su guje wa irin waÉ—annan abubuwa.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment