Siffofin Wanda Ake So A Aura Tsakanin Mace Da Namiji

Siffofin Wanda Ake So A Aura Tsakanin Mace Da Namiji
Siffofin Wanda Ake So A Aura Tsakanin Mace Da Namiji 


Siffofin Wanda Ake So A Aura Tsakanin Mace Da Namiji 


Ko kunsan irin siffofin namijin ko macen da ake son aura? Akwai siffofi da ake so, miji da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin su nemi junansu da aure, don samar da farin ciki da nutsuwa a tsakaninsu, ga siffofin kamar haka:


Siffofin Namijin Da Ya Kamata Mata Su Aura: Yawancin mata idan za su zabi namiji a matsayin abokin rayuwarsu na aure basa duba abubuwan da suka dace, mata sun fi damuwa akan samun namiji mai kudi, kyau, da daukaka. 


Idan mace za ta zabi yana da kyau tafi mai da hankali kan samun namiji wanda yake da wadannan dabi'u:


(a) Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, domin mai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.


(b) Ya kasance ya dan haddace wadansu Ayoyin Alqur'ani, don sukan kara wa bawa Imani, wanda ya haddace ayoyin kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne a wurin Allah.


(c) Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, zagi, takura da cin mutunci ba, a inda babu gaira babu dalili.


(d) Ya kasance yana da kuzarin biyan bukatan Iyalinsa da nemo mata abinci, sutura, wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum tun da Annabi (SAW) yace "Wanda Yake Da Hali Daga Cikin Ku Ya Yi Aure..." [Bukhaqi 5065, Muslim1400].


(e) Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, da samun zamantakewa mai kyau.


(f) Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakanne ta hanyar 'yan uwansa ko zuriyars. Ko da yake haihuwa ta Allah ce, yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma yadda ya so, wani kuma sai ya sanya shi AQIM, kamar yadda yace "YA KAN SANYA WANDA YA GA DAMA AQIM (wanda ba ya haihuwa)" [Shura50].


(g) Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtan juna, don samun zaman lafiya. Anan nake jan hankalin 'yan uwa mata da kada su kuskura su auri mutumin banza, mai halin mutanen iska, don za su shiga mayuwacin halin da zaisa ba za su ji dadin rayuwarta ba har abada. Duba (Sahih Fiqhis Sunnah 3/103-107).


Wadannan sune muhimman abubuwan da ya kamata su sani kan irin mazajen da za su aura, domin shi aure zama ne da ake so a yi na tsawon lokaci ba tare da an samu matsala ba. A darasin mu na gaba za mu kawo muku irin halayen matan da ya kamata maza su aura. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post