Muhimman Abubuwa 4 da Gwamnatin Kano za ta yiwa 'yan Tiktok a Kano |
Muhimman Abubuwa 4 da Gwamnatin Kano za ta yiwa 'yan Tiktok a Kano
Kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi zama da yan Tiktok inda gwamnatin Kano ta yi alkawrin daukar nauyin duk wani dan Tiktok na Kano karatunsu daga Nigeria har zuwa London musamman ga wanda basu da halin biyan kudin karatunsu.
Sannan gwamnatin Kano ta yi alkawrin taimakawa yan Tiktok da jari domin yin sana'a, musamman wadanda suke da sana'ar amma jarinsu ya kare. Yamma Kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa babu wanda za'a baiwa jari har sai ya rubuto tsarin sana'ar da zai yi da kuma yadda zai tafi da ita.
Sannan kuma hukumar ta Hisbah da hadin gwiwar gwamnatin Kano sun yi alkawrin za su aurar da duk yan Tiktok Mazauna Kano da wanda suka daidaita kansu za'a yi musu kayan daki da biyan kudin Sadaki kamar yadda aka yi a auren zawarawa
Ga cikakken bayanin kan zaman da ya gudana tsakanin Hisbah da yan Tiktok
Abubuwan da aka tattauna a wajen taron Hisbah da yan Tiktok da facebook. #abis_fulani #hausa #nigeria #kano pic.twitter.com/74ppz6sUGJ
— Abubakar Sadauki👑👑 (@abis_fulani) November 6, 2023