Mai Gadin Dake Kula Da Kabarin Manzon Allah (SAW) Ya Mutu |
Abdou Ali Idris Sheikh Mai Gadin Dake Kula Da Kabarin Manzon Allah (SAW) Ya Mutu
Agha Abdou Ali Idris Sheikh wanda ke kula da kabarin Manzon Allah (SAW) a Masallacin madina ya rasu. Yana daga cikin mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kula da hidima a Masallacin Manzon Allah (SAW) dake garin madina.
Cikin shekaru 10 da suka gabata Abdou Ali Idris Sheikh shine na uku da suka mutu. A baya yawan masu aikin Agha ya haura mutum dubu daya, amma a halin yanzu wadanda suka rage a raye ba su fi biyar.
Tags:
Labaran Duniya