Ku Kauracewa matar dake da wadannan halayen guda biyar

Ku Kauracewa matar dake da wadannan halayen guda biyar
Ku Kauracewa matar dake da wadannan halayen guda biyar 


Halayen mata marasa kyau da ya kamata maza su Kaurace musu. 


Akwai matan da suke da wasu mugayen halaye wanda idan namiji bai kaurace musu ba zai iya shiga wani hali. Ga wasu daga cikin halaye na mata guda biya da za ku Kauracewa. 


1) Mace ta farko halinta shine, macen da ba ta karbar umarni sannan kuma bata karbar gyara. A duk lokacin da akai mata umarni ko gyara bata karba, mace mai irin wannan halin yana nuna ita mai girman kai ce. Idan baka fita daga sabgarta ba kaima za ta gurbata ka.


2) Matar dake da zafin rai da saurin fushi, wacce koda yaushe take sakaka cikin bacin rai, wannan tana nuna maka cewa idan baka fita daga rayuwarta ba zata iya zama karshen ka. 


3) Macen da bata mutuntaka da girmamaka, irin wannan macen tana nuna maka kwata-kwata ita ba bangaren rayuwarka bace. 


4) Matar dake yin muamala da maza a matsayin abokai, wannan mazan ba kowa bane sai masu maye gurbin ka. Irin wannan macen koda ka aureta Kada ka yi tunanin kai kadai ne ke yin tarayya da ita


5) Na biyar shine matar da batada godiya komai girman abu komai kankantarsa za ta ganshi a raine kuma a wulakance, irin wannan matan komai girman abu za ta ganshi a wulakance babu daraja, wannan macen tana nuna farashin abubuwa ta sani ba Kimar abubuwa ba.


Wannan sune halaye guda biyar na mata da za ku Kauracewa, da fatan maza za su kula sosai da irin matan da suke yin soyayya dasu. Yana da kyau ka fahimci halayen mace da irin tarbiyarta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post