Hotuna: Yadda Kashim Shettima Yayi Taro da 'yan Kannywood |
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima Yayi Taro da yan Kannywood
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi wata ganawa da jaruman Kannywood, bayan taron tattaunawa kan fasaha, da al'ada da ƙirƙire-ƙirƙire don ci gaban tattalin arziƙi a Abuja.
Zaman ganawa da Kashim Shettima yai da yan kannywood na zuwa ne kadan bayan kwana biyu da rasuwar fitaccen darakta a masana'antar ta Kannywood Aminu S Bono.
Hotuna na ta yawo a shafukan social media na ganawar da mataimakain shugaban kasa yai da jaruman Kannywood wanda suka hada da Ali Nuhu, Rahama Sadau Nuhu Abdullahi, Ado Gwanja da sauransu.
Rahama Sadau tare da Kashim shetima |
Babbar jarumar Kannywood Rahama Sadau ita ta wallafa hotunan a shafinta na Twitter tare da wallafa bayani Kannywood dalilin ganawar da sukai da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Ku Kalli Hotunan Yadda Aka Gudanar da taron
I engaged in a productive round table discussion with my principal the Vice President of the Federal Republic of Nigeria, a dexterous leader, a technocrat per excellence in life and deeds His excellency Dr. Senator Kashim Shettima at the just concluded creative stakeholder round… pic.twitter.com/NwIIEXoP0Z
— Rahama Sadau ✨ (@Rahma_sadau) November 22, 2023