Amfanin tsarki da kanunfari |
Amfanin tsarki da kanunfari na magance cututtuka irin na infection dake yin tasiri a gaban mata
Kanunfari na daga cikin abubuwan dake tasiri wajen magance matsalolin infection dake damun mata. Yin tsarki da ruwan Kaninmfari na bayar da gudunmawa sosai wajen kashe infection a jikin mace.
Amfanin tsarki da kanunfari |
Mata na yin amfani da Kanimfari ta hanyoyi daban-daban, amma mafi muhimmanci shine kanunfari ana amfani dashi wajen tsarki domin kashe kwayoyin cutukan dake damun mata a al'aura. Tsarki da kanunfari na taimakawa wajen yin maganin infection.
Yadda Ake Yin tsarki da kanunfari
Ki ganyen magarya da Kaninmfari da tsaftataccen ruwa ki tafasa, ki zuba a buta ko flast. Za ki yini kina yin tsarki da wannan ruwan Kaninmfari da kika dafa. Sannan Kuma za ki iya daka garin kanimfari ki hadashi da totuwar raken da kika sha ya bushe sai ki samu farin miski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da totuwar raken da kuma muskin, idan ya bushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi. Wannan kada ku yi wasa dashi domin yana magance cututtuka musamman na infection dake damun mata.