Domin Ma'aurata Yadda Za Ki Tsokano Sha'awar Mijin Ki

Domin Ma'aurata Yadda Za Ki Tsokano Sha'awar Mijin Ki
Domin Ma'aurata Yadda Za Ki Tsokano Sha'awar Mijin Ki 


Domin Ma'aurata Yadda Za Ki Tsokano Sha'awar Mijin Ki 


A yau inaso na tabo abin da ya shafi yadda ake tsokano sha'awa a auratayya tsakanin ma'aurata da fatan za ku amfana daga abubuwan da za mu yi bayani.


Da yawa daga cikin mata suna daukar cewa yin wasa da motsa sha'awa aikin mijine shi kadai, duk matar da take da irin wannan tunanin to ta ba ta kan hanya a fagen soyayyar zaman aure.


Kuma ki sani wata zata iya kwace miki miji cikin sauki domin galibin maza sunfi so da karkata wajen matar da take yi musu wasa iri-iri . Don haka ina Kira da mata kar ku ji kunya ko gudun kar mijinki yace kina da jaraba, ba haka bane kar kiyi wannan tunanin. Kisani cewa mu'amular aure ibada ce kuma duk sanda zaki yiwa mijinki wasa lokacin saduwa kema fa kina samun wani kaso na jin dadi da nishadi. 


Yadda Ake Tsokano Sha'awa A Yayin Kwanciyar Aure 


Kamar yadda nayi bayani tun a farko muna bayani ne akan yadda ake iya tayar da sha'awa a lokacin kwanciyar aure tsakanin ma'aurata. 


Amma kafin mu fara 'yar uwa ina so ki sani idan akazo irin wannan harkar cire kunya ake yi a ajiye gefe, dalilin da yasa nace haka shine abinda ke cutar da matan aure da yawa shine kunya, mun san kunya ado ce ga mace, amma ba a shimfidar miji ba, idan akazo shimfida, a ajiyewa akeyi har sai komai ya kammala. 


Da anyi magana akan kwanciyar aure sai a ji mata na cewa wlh ni ba zan iya ba kunyar shi nake ji, amma za ta iya tsayawa a gabanshi yana fada tana fada anan ba ta jin kunya sai wajen kwanciya, don haka mata a kiyaye. 


Hanyoyin Yadda Ma'aurata Za Su Tsokano Sha'awa 


Sirrin yadda zaki kwanta da mijinki ki gamsar dashi ke ma kuma ki gamsu. Da yawan lokaci zaki samu mace bata da aiki sai amfani da kayan mata ko nawa ne zata iya kashewa ta saya, wadanda suka dace da wadanda basu dace ba, har ta jawa kanta wata cutar, garin neman kiba a samo rama.


Tabbas kayan mata gaskiya ne kuma suna bada gudunmawa sosai wurin tsokano da sha'awa, amma ance in kana da kyau ka kara da wanka, kuma yanzu komai na duniya an samu cigaba ilimin jima'i kullum kara bincike ake yi a kanshi. Sau da yawa ana samun korafi  daga wasu matan cewa su sun kasa tayar da sha'awar mazajensu wanda hakan ke sa su neman magunguna.


Idan mace na son tsokano da sha'awar mijinta ba sai ta wahalar da kanta da shan magunguna ba babban abinda ya kamata mace ta yi shine ta tabbatar tana da tsafta kuma ba iya tsatar jiki ba har tsatar gida musamman inda kike kwanciya da mijinki.


Ki tabbatar kina da kaya masu matse jiki wanda idan kika saka za su tsokano da sha'awar mijinki. Kuma ki tabbatar kina saka turare masu tsokano da sha'awa wanda ko mijinki baida bukatar ki wannan turaren zai iya saka shi ya tayar masa da sha'awa.


Wannan sune kadan daga cikin yadda mata za su yi domin su tsokano da sha'awar mazajensu. Da fatan mata za su yi amfani da wadannan hanyoyin domin inganta zamantakewar aurensu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post