Dalilan Mutuwar Auren Jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya |
Wata majiya mai tushe ta Bayyana Dalilan Mutuwar Auren Jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya
Rahotonnni na ta yawo a shafukan social media kan mutuwar auren tsohuwar jarumar Kannywood Aisha Aliya Tsamiya duba da irin sabbin hotunanta da suke ta yawo a shafin Tiktok da suke nuni ba mai aure bace. Wannan dalilin na ganin hotunanta yasa mutane suka fara yin shakku kan aurenta.
Shafin mujallar film magazine ya tabbatar da wata majiya mai karfi ta bayyana musu cewa auren jarumar ya mutu tun da dadewa tun kusan watanni hudu da suka gabata wanda aka ce dama sun dade suna samun matsala tsakanin su.
Majiyar ta kara da cewa tun farkon auren nasu jaruma Aisha Aliyu ke fuskantar matsala da mijinta wanda ba'a yi tsammanin auren nasu zai kai lokacin da suka rabu ba. An ce tana zargin mijinta da yin soyayya da wasu matan wanda ita kuma ba ta amince da hakan ba.
Auren Aisha Aliyu Tsamiya da mijinta Alhaji Buba Abubakar bai wuce shekara da yi ba domin an yi bikin auren a shekarar 2022 ne wanda kuma yanzu auren ya zo karshe.
Yanzu dai hankula sun karkata kan jaruma Aisha Aliyu, shin za ta kara yin wani auren ne ko kuma za ta dawo harkar film a ci gaban daga inda aka tsaya, lokaci ne dai zai tabbatar da hakan.