Amfanin Hulba A Nono |
Sirrin Amfanin Hulba A Nono Mace
kamar yadda mu ka san Hulba kalma ce ta larabci, da harshen turanci ana kiran ta da 'Fenugreek'. Hulba wani tsiro ne mai matukar amfani ga lafiya, kuma shekaru aru-aru da su ka shude al'umma ke yin amfani da ita don samun waraka daga wasu matsalolin lafiya.
Mata da dama a sassan duniya na amfani hulba don gyaran nono. Hulba tana bayar da gudunmawa sosai wajen kara girma da lafiyar nono ga mata.
Amfanin Hulba Don Gyara Nonon Mace
Amfanin hulba don gyaran nono; Bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da hulba don gyaran nono. Dalili kuwa shine, hulba na sanya fata da tsokar dake kewayen nonon mace su buɗe, hakan sai ya sa nonon ya ciko ɓulɓul abin sha'wa, musamman idan nonon ya kasance da girmansa amma ya kwanta.
Abubuwan da ake bukata sune; garin hulba da garin Shammar da kuma zuma.
Yadda Za'a Hada Hulba Don Yin Maganin Nono
Za a samu garin hulba da garin shammar. Ki ɗebi cikin ƙaramin cokalin guda daya 1 na garin hulbar sai a zuba cikin kofi mai tsafta da aka tanada, sannan a zuba garin shammar, shima cikin ƙaramin cokali guda, sai a gauraye su waje guda. Daga bisani a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara a kan garin hulba da na shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti 10 sai a tace da rariya, bayan an tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a sha.
Daga bisani sai a shafa man hulba ga nonon. Wajen shafawa akan nonon a tabbatar an murza man hulbar sosai akan nonon gaba daya yadda zai shiga fatar nonon da kyau. Za a sha wannan hadin sau biyu a rana, wato da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin hakanan za a shafa man hulbar a kan nonon, shi ma ya zama sau 2 kenan.
Yadda za ki gane maganin na amfani shine, ta hanyar jin nononki na kara nauyi, alamar ya fara cikowa kenan.
Amfanin Hulba A Nono Ga Mata Masu Shayarwa
Hulba na maganin rashin ruwan nono ga mai shayarwa; A wasu lokutan, akan samu mace ta haihu amma sai ta samu karancin nono. Yin amfani da hulba zai samarwa da mai shayarwa ruwan nono, kuma zai taimaka wajen girman jaririnta.
A kasashen da ke nahiyar Asia, mata kan yi amfani da hulba don maganin matsalar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Masana sun ce, hulba na taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mata ma su shayarwa ne, sakamakon wani sinadari mai suna 'phytoestrogen' da ta ke kunshe da shi. Ana samun wannan fa'ida ta hulba ne, ta hanyar shan ta cikin ruwan shayi.
Ko kuma, mace ta samu 'ya'yan hulba ta dafa da man Ridi ta dinga ci har tsawon kwana 3, sannan ta ke shafa man hulbar a nononta, za'a samu biyan bukata. Domin kuwa za ta samu ruwan nono da zai wadatar da jaririnta, kuma ya kasance cikin koshin lafiya.