Amfanin gishiri a gaban mace |
Amfanin gishiri a gaban mace
Shin ko kunsan yadda amfanin gishiri yake a gaban mace? Kamar yadda aka sani gishiri na maganin cututtuka da dama musamman cutuka irin na Bacteria da suke damun mata.
Ana yin amfani da gishiri haka don magance kaikayin gaban mace domin yana aiki sosai wajen kashe dukkan wasu cutuka na bacteria. Yin amfani da gishiri a gaban mace yana iya Kawar da duk wasu cututtuka dake damun gaban mace.
Yin amfani da gishiri a gaban mace ba wai kawai saka shi ba. Kada a shafa gishiri kai tsaye a kan gaban mace, sannan a kula sosai a yayin da za'a yi amfani da gishiri a gaban mace, kada a yi amfani da shi idan akwai ciwo a gaban mace.
Yadda Amfanin Gishiri Yake A Gaban Mace
Idan mace na fama da kaikayin gaba, ta samu gishiri a zuba a mazubi mai kyau a kara ruwa, an fi son a yi amfani ruwan dumi domin gaban mace ya fi son ruwan dumi, sai a zuba gishiri kadan, za a dibi wannan ruwan ana yin tsarki dashi a gaba mace. Sannan kuma, ana iya samun ruwan dumi a zuba gishiri a ciki, sai a zauna a cikin ruwan na tsawon mintuna 15 zuwa 20.
Baya ga maganin kaikayin gaba, yin amfani da ruwan gishiri a gaban mace na kuma bada kariya na hana kananan cutuka zama a gaban mace. Sannan a kiyaye, kada a yi amfani da sabulu, ko wasu mai da ba likita ne yace a yi amfani dasu ba wajen wanke gaban mace, yin hakan ka iya kara yawan kaikayin da ake ji.