Amfanin Ganyen Zaitun Domin Sabuwar Amarya |
Duk macen da za'a yi aurenta cikin wata 1 ta yi kokarin yin amfanin da ganyen Zaitun Domin jindadin kwanakin amarcinta
Iyaye shin kusan amfanin ganyen Zaitun da ya dace ku yiwa ya'yan ku mata aiki dashi a lokacin da suke shirin yin aure? Idan baku sani ba ku Karanta wannan rubutun har zuwa karshe.
Duk iyayen da suke son su aurar da yarinyar su yana da matukar muhimmanci su yi amfani da ganyen Zaitun a turara mata Jikinta dashi, domin zai taimaka mata a kwanakin amarcin date za ta yi da mijinta.
Yadda Za Ku Yi amfani da ganyen Zaitun.
Idan ya rage wata daya a yi bikin 'yarki, Ki samu ganyen Zaitun ki wanke ki tafasa shi, yarinyar za ta shiga cikin ruwan tsirara ta zauna cikin ruwan har tsawon minti 30 har zufa a dinga fita daga Jikinta sannan ta fita.
Amfanin da ganyen Zaitun ke yi ga jikin mace ya wuce a fadi, kai har macen da ta yi shekara 50 tana iya yin amfani da wannan ganyen named Zaitun domin zai taimaka mata wajen zamantakewar aurenta.