Abubuwan Dake Jawo wa Mace Rashin Sha'awa

Abubuwan Dake Jawo wa Mace Rashin Sha'awa
Abubuwan Dake Jawo wa Mace Rashin Sha'awa 


Abubuwan Dake Jawo wa Mace Rashin Sha'awa 


Akwai mata da yawa dake korafin rashin sha'awa musamman a lokacin saduwa. Sai dai da yawa daga cikin su basu san musabbabin abubuwan dake jawo musu rashin sha'awar ba. A wannan rubutu na yau mun tattaro muku wasu daga cikin abubuwan dake jawo wa mata rashin sha'awa. 


1- Matsalolin Mara Da Mahaifa 

Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura, na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.


Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan ƙananan ƙuraje acikin farji na sanya mace taji zafi yayin  jima'i, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen a cikin al'aura ba. sai dai su ce su na jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda gugar da ake yi musu yayin saduwa, sai wurin ya zama ya yi rauni.

  

2- Budewa 

Budadden gaba ga mace na daga cikin abinda ke jawo wa mace rashin sha'awa. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu samu gamsuwa ba da kyau, sannan macen baza ta iya jin ƙololuwar dadi ba shi ma namijin haka saboda rashin haduwar fata da fata yadda ya kamata.


3- Kaciyar Mata 

Idan aka samu matsala wajen yiwa mace kaciya, ya zamanto an yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na jawo rashin sha'awar mace idan ta girma. Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i, domin kuwa beli shi ne matattarar jin dadin jima'in mace.


4- Magunguna 

Yin amfani da magunguna ba bisa ka'ida ba. Yawaita shan magunguna barkatai kan iya ragewa mace sha'awa ko kuma ya sa ta dauke baki daya. Wani lokacin kuma ko da bisa ka'ida aka sha maganin to zai iya yiwuwa daga cikin side effect dinsa shi ne yana dauke sha'awa zuwa wani lokaci.


6- Rashin Abinci Mai Gina Jiki 

Abinci mai gina jiki na nufin abincin da ke dauke da sinadaran da jikin mutum ke bukatarsu, to shi ne mai gina jiki a wajensa. Idan mace ba ta samun ingantaccen abinci to za ta iya samun matsalar rashin sha'awa sosai. 


7- Rashin Fahimtar Yanayin Mace 

Wata matar ba wai sha'awar ce ba ta da ita ba, a'a. Ita kanta ba ta fahimci abinda zai sa mata sha'awar ba ne, shi ma mijinta bai fahimce ta ba, sai a tafi a haka, a matsayin ba ta sha'awa.


8- Wasa Da Gaba 

 Wasa da gaba wanda akafi sani da istimna'i. Idan mace na wasa da farjinta yana iya haifar mata da rashin sha'awa. Idan kinsan kinayin wasa da alaurarki domin ki biyawa kanki bukata sai kiyi kokarin dainawa.


Wadannan sune abubuwan dake jawo rashin sha'awa ga mata, da fatan za ku yi kokarin kulawa da abubuwan da muka bayyana domin kare lafiyar jikin ku. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post