Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Salma ta shirin Kwana Casa’in

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Salma ta shirin Kwana Casa’in

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Salma ta shirin Kwana Casa’in 


Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Salma ta shirin Kwana Casa’in 


Aisha Saleh Kyari wacce aka fi sani da princess Mufida kuma Salma a cikin shirin kwana casa'in. Aisha Saleh Kyari yar asalin jihar Borno ce. Babanta bature ne dan asalin kasar Australia babarta kuma 'yar Borno.


Aisha Saleh Kyari da aka fi sani da Salma an haife ta a garin Maiduguri na jihar Borno, ta yi karatu tun daga nursery school a birnin Maiduguri sannan kuma ta yi primary, secondary da polytechnic a birnin Abuja inda ta karanci art & music.


A tattaunawar ta da bbc Hausa,Salma kwana casa'in, ta bayyana cewa film din ta na farko shine kwana casa'in wanda aka gayyaceta don yin wani role a cikin film din.


Salam kwana casa'in ta ce tun tana yarinya a secondary school take sha'awar shiga harkar fina-finai wanda sai da ta fara hip-hop sannan kuma daga baya ta koma Finafinai.


Salma Ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a farko kafin ta samu karbuwa a film din kwana casa'in domin asali ba role dinta bane wata ce ke yi role din amma kuma daga baya an yi accepting dinta.


Salma kwana casa'in ta bayyana cewa abinda yafi bata mata rai shine karya, ta ce bata son karya ko kadan. Idan mutum zai fadamata abu to ya fadamata gaskiya.


Role din da Salma take yi a shirin kwana casa'in mai dogon Zango shine bata son rashin gaskiya kuma bata goyon bayan iyayenta kan tauyewa al'umma hakkin su. Kullum tana yin fada ne da iyayenta don su yi gaskiya sannan mulkin da suke yi ya kasance na gaskiya ba tare da cutar da wani ba.


Ga cikakken bidiyon hirar Salma kwana Casa’in


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post