Abdul Amat Mai Kwashewa ya saya wa Iyalan marigayi Aminu S Bono sabon gida |
Producer Abdul Amat Mai Kwashewa ya saya wa Iyalan marigayi Aminu S Bono sabon gida
Babban Producer a masana'antar Kannywood wanda aka fi sani da ABDUL AMART MAI KWASHEWA, ya siyawa iyalan darkata Aminu S Bono muhalli (GIDA) kuma ya nemi a boye ba tare da ansani ba amma duk da haka labarin ya fita.
Dangin marigayi Daraktan Fina-finan Hausa Aminu S. Bono sun tabbatar wa da Freedom Radio cewar Mashiryin Fina-finan nan Abdul Amat Mai Kwashewa ya saya wa Iyalan marigayin gida.
Kafin rasuwar Marigayi Aminu S Bono ya kasance daya daga cikin manya-manyan Darektocin kamfanin Abnur Entertainment And General Media Solutions.
Rasuwar Bono ta girgiza masana'antar Kannywood. Ya dade yana cikin masana'antar inda ya bada umarnin finafinai da sukai tasiri da daukaka.