Yakin Karbala Wanda shi ne yayi Sanadiyar shahadar Husaini bn Ali (AS) |
Yakin Karbala Wanda shi ne yayi Sanadiyar shahadar Husaini bn Ali (AS)
A Rana 10 Ga Watan Oktoba 680 MIladiyya akayi Yakin Karbala wanda shi ne wanda yayi sanadiyar shahadar Husaini bn Ali (AS).
Yakin Karbala, wanda aka Gabza a ranar 10 ga Oktoba, 680 wanda yayi daidai da10 ga Muharram, shekara 61 bayan hijra, yakin soja ne in da wata karamar runduna karkashin jagorancin al-Husayn bn Ali (AS) jikan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa Alihi Wasallama) kuma dan iman Ali (AS), khalifa na hudu, ya kasance da runduna wacce halifan Umayyawa Yazid na daya ya aika, sun yi galaba a kan Imam Husaini (AS) da yan Rakiyarsa, inda sukayi musu kisan kiyashi.
A lokacin da imam Husaini (AS) ya ki mika wuya, sun kashe shi da tare da ‘yan rakiyarsa, kuma aka aika kan imam Husaini (AS) zuwa wajen Yazid a Damascus (yanzu a Syria). Domin tunawa da shahadar Hussaini (AS), musulmi ‘yan Shi’a su na raya kwanaki 10 na farkon watan Muharram (ranar yakin da aka yi a kalandar Musulunci) a matsayin ranakun makokin (Ashūrā’).