Satar Rake ta janyo an yiwa wani matashi Bulala goma sha biyar a Kano |
Satar Rake ta janyo an yiwa wani matashi Bulala goma sha biyar a Kano
Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Kwana Hudu a Jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari'a Khadi Nura Yusuf Ahmed, ta bayar da umarnin a yi wa wani matashi mai suna Yakubu Haruna mai shekaru 25 bulala 15 sakamakon satar rake.
Jami'i mai gabatar da ƙara, Aliyu Abidin Murtala, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Abdullahi Muhammad, mazaunin Rimin Kebe, ya kai kara ga ofishin baturen ƴansanda da ke Zango cewa wanda ake kara ya sace masa sandunan rake guda biyu, laifin da ya saba da sashe na 133 na kundin laifuka na Penal Code na Jihar Kano.