maganin Karin Ni'ima |
Maganin Karin Ni'ima Ga Mata
Kamar yadda yan uwa suka bukata, a yau za muyi bayani akan yadda za'a hada magani wanda yake karawa mata ni'ima kuma wannan hadi yana kara lafiyar jiki ga ma'aurata.
Abinda Za'a Nema domin yin wannan maganin sune kamar haka.
1. Dabino mai kyau
2. Girfa(Cinnamon)
3. Bushasshiyar Citta(dry Ginger)
4. Zuma mai kyau.
Yadda Za'a Hada maganin.
Da farko za'a yi blending din dabinon da ruwa kadan a zuba a cikin wani mazubi mai kyau, sannan ka kawo garin Girfa kamar chokali 10 Garin Citta chokali 5 a zuba a ciki sai a kawo Zuma kamar Kofi daya da rabi a Zuba akai a cakuda sosai sannan a rika shan chokali 2 sau 3 a rana. Wannan hadin maganin zai taimaka wajen kara samun Ni’ima.
Allah yabamu lafiya dazaman lafiya