Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya - Android Pols

Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya
Dauda Kahutu Rarara & Aisha Humaira 


Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya


Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya sanya gasar wata sabuwar waka da yayi akan shirin gwamnatin tarayya na ƙidaya da za'a gudanar a farkon shekarar 2024, inda ya bayyana muhimmancin ƙidaya ga yan ƙasa Nigeria. 


Aisha Humaira wacce abokiyar aikin Rarara ce, tayi bayanin yadda ƙidayar za ta taimaka a sha'anin tsaro, tare da bayani akan yadda gasar za ta kasance da kuma irin kyaututtukan da za'a bayar ga wadanda suka shiga gasar, da suka hada da Mota, Babur da kuma kuɗi. 


Sai dai kuma gasar bata samu karɓuwa ga ma'abota shafukan sada zumunta musamman TikTok ba, inda wasu jaruman dandalin ke ganin Rarara bai shiga lamarin kira ga gwamnati akan matsalar tsaro da ake shan fama a Arewacin Nigeria ba, saboda haka a yanzu shima ba zasu karɓi bukatarsa ba.


Me zaku ce akan wannan lamari? 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

2 Comments

Previous Post Next Post