sayyada sadiya haruna and Al'amin G-Fresh |
Idan shekara 1000 za ayi, bazan saki mata ta sayyada sadiya haruna ba, don ina son ta har yanzu - G-Fresh
Mawaƙi Abubakar Ibrahim (G-Fresh Al-amin, Kano State Material), yace ko shekara dubu za ayi nan gaba, bazai saki matarsa Sadiya Haruna ba, kuma har yanzu ana kan batun sulhu ne a Kotu.
Tun bayan samun saɓani tsakanin ma'auratan, aka gaza gane hakikanin abinda ya faru, domin ita Sayyada Sadiya Haruna ta ce sun rabu da G-Fresh, amma kuma ya kafe akan cewa bai sake ta ba, kuma bazai sake ta ba.
Komai zai zo karshe ne idan lokacin da kotu ta kammala sauraro tare da yanke hukunci akan shari'ar.