Idan ɗanka ko ƴarka sun kai shekarun farko na tashen balaga, ku kula da wadannan abubuwan

Idan ɗanka ko ƴarka sun kai shekarun farko na tashen balaga, ku kula da wadannan abubuwan
Idan ɗanka ko ƴarka sun kai shekarun farko na tashen balaga, ku kula da wadannan abubuwan   


Idan ɗanka ko ƴarka sun kai shekarun farko na tashen balaga, ku kula da wadannan abubuwan

 

Balaga tana faruwa ne ga maza da mata a shekarun farko, idan mace ne balaga tana zuwar mata daga shekara 11 zuwa 15 shi kuma namiji daga shekara 15 zuwa 18. 


Yawanci wasu yaran suna jin tashen balaga a wannan shekarun nasu wanda idan ba'a kula ba suna iya fadawa cikin mawuyacin hali. Akwai abubuwan da ya zama wajibi iyaye su kula dasu ga yaransu a irin wannan shekaru na tashen balagarsu kamar haka.


1. Duk lokacin da yaro ko yarinya suka kai matakin tashen balaga wato "early adolescence", musamman daga shekara 11, 12 zuwa 13, 18, To wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga yara da iyayensu.


2. A lokacin ne yaro yake samun zama na gari ko na banza, me amfanar da al'umma ko me cutar da su.


3. Yaro ya fi tasirantuwa da abokansa ko kawayenta fiye da malamansa ko mahaifansa.


4. Yaro yana jin shima daidai yake da kowa a duniya, kuma zai iya yin komai kamar yadda kowa yake yi, haka ita ma yarinyar.


5. A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon mahaifansa akansa. Yana son dakinsa daban, wajen kwanciyarsa daban, abinci, kayan sakawa da aski sai wanda ransa yake so.


6. A lokacin ne yake jin karfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa. 


7. A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga, ba kan gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tinaninsa), idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi/ita.



MAFITA


1. A shekarun balaga Iyaye su ja yaronsu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi masa gyara da tarbiyyarsa.


2. Kar su nuna masa karfi ko iko, domin zai iya baudare musu, a karshe ya haifar musu da hawan jini.


3. A kula sosai da su waye abokansa, ko kawayenta. A hada shi da na gari, a raba shi da na banza.


4. A samar masa da aikin yi, wajen nuna masa yadda zai dogara da kansa (koda kuwa dan masu kudi ne shi).


5. A tsara masa ayyukan da zai ke yi a kullun tun daga safe zuwa rana, i.e. makaranta, bacci, cin abinci, ziyara, hutu, da sauransu.


6. Iyaye su zama abokan 'yayansu wajen bincikar matsalolin 'yayan, da magance musu ita.


7. Ka da a hana yaro wani abu, face sai a maye masa gurbinsa da wani, idan ba haka ba, to zai yi abin da ya fi wanda aka hana shi muni.


8. Kar ayi amfani da karfi, da duka, da tsattsauran hukunci wajen ladabtar da shi, har sai idan abu ya ta'azzara, sai a je da shi "guidance and counseling office" domin neman shawarwari.


9. Ake tunatar da su ayoyin alqur'ani da hadisan Manzo (SAW) da sukai magana akan biyayyar iyaye, da mahimmancin zama nangari


10. Sannan ake hadawa da addu'ar nema musu shiriya da nagarta a wajen Allah (SWT)

Wallahu a'alam.


Wadannan sune abubuwan da ya zama wajibi duk iyaye su saka ido ga yaransu domin kaucewa abinda zai iya faruwa dasu na faɗawa halaka.


Bukhari Musa Adam

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post