Daurin Zawarawa A Kano |
Hotuna: Yadda Aka Gudanar da Walimar Daurin Auren Zawarawa A Kano
Bayan daura auren zawarawa da yan mata da gwamnatin Kano ta yi a ranar Juma’a 13/10/2023 an yi taron walima a gidan gwamnati a ranar Asabar 14/10/2023.
Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Jigawa, Malam Umar Namadi sun halarci walima/ liyafar daurin aure (Auren Gata) na Ma'aurata 1800 wanda gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyi.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fara kaddamar da wannan shiri a lokacin gwamnatinsa a wani bangare na shirin inganta rayuwar jama'a a jihar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Bishop Isaac Idahosas, shugabannin jam’iyyar da fitattun malaman addinin musulunci a fadin Najeriya.
Ga hotunan Yadda walimar ta kasance