Dubu Ta cika: An Dakatar Da Farfesan Dake Tilastawa Dalibansa Mata Lasar Gaban sa |
Dubu Ta cika: An Dakatar Da Farfesan Dake Tilastawa Dalibansa Mata Lasar Gaban sa
Jami’ar Calabar a jihar Cross Rivers ta dakatar da daya daga cikin manyan malamin ta daga Jami’ar. Jami’ar ta dakatar da farfesa Cyril Ndifon bayan an gano yadda yake bibiyan dalibansa ya yi lalata da su da hana su kammala karatunsu a lokacin da ya kamata.
Asirin wannan malami ya fara tonuwa a lokacin da wata dalibar jami’ar ta kai karar farfesan cewa ya nemi yi yi lalata da ita a ofis dinsa.
Bisa ga karar da dalibar ta kai ta ce ta fara haduwa da Ndifon lokacin da ta nemi ta canja fannin da take karatu daga fannin ‘Conflict Studies’ zuwa fannin Shari’a (Law).
Ta ce Ndifon ya ce idan har tana so ta dawo fannin shari’a domin ta ci gaba da karatu ta lasar masa azakarinsa.
Dalibar ta ce hakan ya faru yayin da ta shiga ofishinsu domin ya saka mata hannu a takardan canja fannin karatunta.
Ta kuma gabatar da sakonnin tes da na murya da shi farfesan ya rika mata da ya ke mata barazana don kada ta kai karar sa.
Bayan haka ne jami’ar ta kafa kwamitin mutum bakwai domin gudanar da bincike kan zargin da dalibar ta yi kan farfesan
A zaman da kwamitin ta yi wasu dalibai mata sun fito da hujjoji da bayanai kan yadda Ndifon ya yi kokarin yin lalata dasu kuma ya hana su kammala karatunsu a lokacin da ya kamata.
Da dama daga cikin matan sun ce farfesan na aikata wannan ta’asa ne a cikin ofishin sa. Daliban sun ce a duk lokacin da suka shiga ofishin Farfesan sai ya yi mazamaza ya kulle kofar da mukulli ya zaro azzakarinsa ya mika musu su rika lasa. Sun Kuma ce idan daliba ta ki sai ya yi mata barazanar cewa zai kayar da su a jarabawa.
Sakakamon binciken da kwamitin ta gabatar
Kwamitin ta ce ta gano yadda farfesan ke amfani da ikon ofishinsa domin yin lalata tare da hana dalibai su kammala karatunsu a lokacin da ya kamata.
Kwamitin ta bada shawarar a tilata wa farfesan ya biya daliban miliyan 3 din da suka biya wajen siyan takardun da ya siyar musu.
Kwamitin ta kuma yi kira ga jami’ar da ta hana malamai ganawa da daliban su a lokutan da basu kamata ba.
Kwamitin ta kuma ce daga yanzu kamata ya yi duk malamin da zai hadu da dalibinsa a ofis su rika barin kofar ofishin a bude.