Auren gata na gwamnatin Kano bai yiwu ba domin ba'a bi ƙa'idar addini ba - Garba Izala

Auren gata na gwamnatin Kano bai yiwu ba domin ba'a bi ƙa'idar addini ba - Garba Izala
Garba Izala 


Auren gata na gwamnatin Kano bai yiwu ba domin ba'a bi ƙa'idar addini ba - Garba Izala 


Tsohon kwamishinan ma'aikatar harkokin albarkatun ruwa na jihar Kano a Gwamnatin da ta gabata, Garba Yusuf Izala, ya soki batun Auren gata da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta gudanar karkashin kulawar hukumar Hisbah, inda yace auren ya saɓa da ƙa'idar addinin musulunci. 


Cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sadarwar zamani, Garba Izala yace sadakin N50,000 da gwamnatin ta bayar bai kai abinda aka kayyade ba, saboda haka ko dai gwamnati ta nemo ragowar kuɗin ko kuma Angwayen su cika kuɗin da kansu, ko kuma nan gaba idan an haifi 'ya'ya su biya cikon kudin.


Wata tambaya da mai nadar bidiyon yayi masa, yace akwai wata kalma da ake kiran 'ya'yan da aka same su a irin haka, matukar dai ba'a warware lamarin ba. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post