Alamomin Kanjamau Na Gaskiya |
Alamomin Kanjamau Na Gaskiya
Da farko dai kalmar AIDS na nufin Acquired Immunodeficiency Syndrome, ma’ana cuta mai karya garkuwar Jiki da take yaduwa. Ita kuma kalmar HIV na nufin Human Immunodeficiency Virus (ma’ana Virus mai karya garkuwar Jikin dan Adam). Ita AIDS ita ce cutar, HIV kuma shine mai jawo cutar ko kuma virus din.
Cutar AIDS ko Kanjamau cuta ce ta mutane mai karya garkuwar jiki (Immunodeficiency syndrome) wadda ta ke faruwa sakamakon shigar kwayar halittar HIV virus, a cikin jikin mutum.
Alamomin Kamuwa Da Cutar kanjamau Na Gaskiya HIV
Mafi yawan mutanen da su ka kamu da cutar HIV kan ji alamomin mura musamman makonni biyu zuwa shidda bayan daukar cutar. Bayan wannan, bincike ya nuna ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba har sai bayan shekaru masu yawa. Alamomi sun hada da;
-Zazzabi
-Ciwon wuya
-Ƙuraje a jiki
-Kasala
-Ciwon gaɓoɓi
-Kaluluwa a wasu sassan jiki.
Bayan wadannan alamomin na farko-farko sun bace, ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba. Wanda daga karshe take kai ga mutuwar marar lafiya. Kuma tana yaduwa ta hanyar jima’I da mai dauke da cutar; haduwar jini (ko wani daga ruwan jiki kamar maniyyi) ta hanyar gurbatattun kayan aiki kamar reza, wuka, almakashi, allura, da dai sauransu. Amma dai, kamar yadda alkalumma suka nuna, kashi 95% na yaduwa ne ta hanyar jima’i da mai dauke da cutar.
A wannan lokaci, kwayar cutar tana ci gaba da lalata garkuwar jiki. Da zarar garkuwar jiki ta durkushe, alamomin da za a iya ji su ne:
-Rama
-Gudawa ba kakkautawa
-Zufa cikin dare
-Yawan kuraje a jiki
Manyan cututtuka masu hadari
Gano cutar HIV a kan kari na rage yiwuwar lalacewar garkuwar jiki. Sannan a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.
Alamomin Bayyanar Cutar Kanjamau Na Gaskiya
Bayyanar alamomin Cutar Kanjamau ya kan sha ban-ban a tsakanin mutane. Bayan shigar kwayar cutar virus na HIV, alamomi kan iya fara bayyana daga watanni kadan har zuwa shekaru goma ko sama da haka. Wannan kuma ya ta’allaka da yadda shi virus din ya habaka ya kara yawa, da kuma karfin garkuwar jikin mutum da kuma irin yanayin rayuwarshi. Amma dai alamomi na farko-farko sun hada da yawan gajiya, zazzafi ko masassara, ciwon kaluluwa (lymph nodes enlargement) ko kumburin hamata, kyuibi, mara, da kuma makwallato (sore throat).
Za ka ga mutum ya gaza aikin da a can yakan yi shi cikin sauki, Idan cutar ta ta’azzara, toh, sauran kwayoyin cuta kamar su bacteria da fungi (hunhuna) da kuma tsutsotsin jiki (parasites and worms) za su samu dama su habaka, saboda garkuwar jiki ta yi rauni. Karshe cutuka kamar tarin Fuka, amai da gudawa, kurajen jiki, da kuma kurajen al’aura duk za su bayyana. Akwai dai alamomi barkatai, da za su iya shan banban daga mutum zuwa mutum.
Yaya ake gane mutum yana dauke da cutar kanjamau AIDS
Ana iya ganewa da tabbatarwa ne ta hanyar yin bincike a dakin binciken asibiti, kuma a tabbatar da hakan daga bakin kwararren likita!
Maganin Cutar kanjamau
Maganar gaskiya, har yanzu ba’a samar da shakikin maganin cutar Kanjamau ba. Sai dai akwai magunguna masu karfi da suke rage kaifin cutar, kuma su hana kwayar virus habaka. Amma dai basu kawar da cutar gaba daya. Wani hanzari ba gudu ba, su ma kuma magungunan, suna da illa mai tsanani, domin su kan haifar da wasu cutuka idan aka yawaita shansu. Kuma dole ne a sha su, idan har ana son mutum ya samu sauki-sauki.
Riga kafin daga kamuwa da cutar kanjamau
Haka kuma, kamar yadda ake yi wa cutar kyanda, sankarau, polio riga-kafi, ita Cutar AIDS ba a mata riga-kafi, duk da cewa har yanzu ana kan bincike akan hakan. Amma dai babban riga-kafi da kuma kariya daga Kanjamau sun hada da:
● Alamomin da ke nuni da wata kila cewa mutum na dauke da wannan cuta
■ Zazzabi da ya ki ci ya ki cinyewa.
Idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani a je a yi tes na cutar kanjamau.
Ciwon makoshi, wanda ake kira sore throat, idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya.
■ Kurarraji a fata.
Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima
Kaluluwa
Yawan ciwon jiki da gabobi.
Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba.
Barkewar zawo.
Yawan ciwon kai, maras dalili
Amai ko tashin zuciya.
■ A kula: Ba wai kawai don mutum na daya ko biyu daga cikin wadannan wai lallai yana da cutar ba, a'a. Kawai dai idan sun hadar wa mutum farat daya a jika, masana kan ce a je ayi bincike, ko a tari cutar da wuri, idan har ita ce.
Anan zan tsaya. Ina rokon Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya, Ya kuma kare mu da duk al’umma daga kamuwa da muyagun cututtuka, Amin.