Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Jaririyar Da Aka Haifa Masa Don Baya Son Haihuwar Mace - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda Wani Magidanci Ya Kashe Jaririyar Da Aka Haifa Masa Don Baya Son Haihuwar Mace




Wani magidanci ya kashe jaririyar da aka haifar Mads domin shi ba ya son haihuwar mace sai namiji.


Wani matashi dan shekara 28 mai suna Misbahu Salisu ya kashe jaririyarsa mai kwana daya a duniya da wani maganin kwari mai suna, saboda ya fi son jariri. 


Lamarin dai ya faru ne a garin Doka Baici da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano.


Hukumar tsaro ta sanar da kama Salisu ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Kano ta hannun mataimakin kwamanda Janar na ayyuka, Dr Mujahid Aminudeen.


Aminudeen ya ce Salisu ya amsa cewa shi ne ya ba wa jaririyar maganin kwari, bayan ya shayar da  mahaifiyarta kwaya a shayi dauke da maganin barci.


Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fi son É—a namiji amma matarsa ​​ta haifi mace, wanda hakan ya sa ya kashe jaririn, cewar jami'in tsaron a cikin sanarwar da suka fitar.


Daga Jarida Tsuntsuwa

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel