Nayi taimako saboda Allah, amma kuma abin ya zame min alaƙaƙai - Aisha Humaira




Jaruma a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Aisha Humaira, ta ce yaron da yayi takanas ta Kano tun daga Bauchi don ganinta, wanda ta taimaka masa har tayi alkawarin ɗaukar nauyin karatunsa, ya zame mata alaƙaƙai.


Aisha Humaira ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, tana mai cewa, ta yiwa yaron goma ta arziki har tayi alkawarin za ta bawa mahaifiyarsa kuɗi domin tayi jari da cigaba da kula da yaron, a lokacin da suka zo Kano da wani makobcinsu domin tafiya da yaron, amma abin mamaki, ance tun a Tasha yaron ya tsere, haka mahaifiyarsa da makobcin suka koma Bauchi ba tare da yaro ba. 


Jarumar tace ta kashe kuɗaɗe sosai akan yaron, kama daga wajen kwana da sauransu, har Wayoyi da siya guda biyu ta bashi tare da mahaifiyarsa, amma ya dawo yace an kwace, haka tasa aka ƙara mayar dashi Bauchi, sai dai kuma an sanar da ita ya ƙara dawowa, har yana hawa Aljanu yana cewa a Kano zai zauna kuma tare da Aisha Humaira. 


To amma Aisha Humaira ta ce dama tun kafin dawowarsa a karo na uku, hukumar HISBAH ta shiga tsakani, duk inda aka sake ganinsa to kada a alaƙanta ta dashi, domin ba zata iya zama tare dashi ba, tace ita ma ba mazauniya bace, sana'arta ba ta zama waje guda bace, saboda haka take kira ga hukumomi da sauran mutanen da zasu iya agaza mata, da su raba ta da wannan yaro

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post