Maryam Ibrahim Shettima (Maryam Shetty)


An haifi Maryam Shettima ce a ranar 8 ga watan Afrilu 1979 a jihar Kano. Yar shekaru 44, 'yar gwagwarmaya ce ta siyasa da zamantakewa, ƙwararriyar likitan motsa jiki, kuma ƙwararriyar 'yar kasuwa ta zamantakewa.


Ta yi digirinta na farko a jami’ar Bayero da ke Kano, in da ta yi karatu a fannin lafiya, in da ta ƙware a fannin kashi.


Ta kuma samu digirinta na biyu a jami’ar Stratford da ke Birtaniya in da ta karanta fannin kula da ƙashi na ɓangaren wasanni.


Maryam ta kasance a cikin likitocin tawagar Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin Landon a shekara ta 2012.


Baya ga wannan, Maryam ta yi kwasa-kwasai da dama a wasu cibiyoyi na ƙasashen duniya, ciki har da Amurka.


A fagen siyasa ma, shigar Maryam ta yi tasiri. Ta kasance memba mai mahimmanci a cikin Tawagar Yakin neman zaben Shugaban Kasa, ta ba da gudanar da ayyuka daban-daban, gami da Ayyukan Fage da Sadar da Dabarun Matasa da Ƙungiyar Yakin neman Shugabancin Mata. Ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a jihar Delta.


Duk da cewa ba ta taɓa yin takara ba, ta kasance ƴar siyasa a a jam'iyyar APC mai mulki.


Ta kasance a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.


Kuma shahararriya ce a shafukan sada zumunta na Najeriya.


Da basirar siyasarta da jajircewarta ga jam’iyyarta, Maryam ta zama fitacciyar Jigo a APC. Gudunmawar da ta bayar ga kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima na da matukar kima, kuma ta taka rawar a zo a gani wajen zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.


Ba irin wannnan gudunmawar  kawai Maryam ta bayar ba. haka kuma Ta samu digirin girmamawa daga jami’ar fasaha ta ESGT da ke jamhuriyar Benin, bisa la’akari da yadda ta yi fice wajen jagoranci da kuma kokarin ci gaban al’umma.


Tun da farko ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, da ingantaccen shugabanci, da shigar mata da tsiraru a cikin al'umma, Maryam na ci gaba da daga muryarta ta hanyar tasiri da farin jini a harkar. 


A ranar 2 ga Agusta, 2023, sunan Maryam Shetty ta shiga cikin sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya nada. Saboda jajircewa da gudunmawar da ta baiwa kasar, ta wakilci Najeriya a zauren Majalisar Dinkin Duniya a kwamitin tabbatar da gaskiya da yaki da cin hanci da rashawa.


Maryam Shetty tayi aure kuma Allah ya albarkace ta da yara. Sai dai ban sami wani bayani a dangane da iyalan Maryam Shetty ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post