Auren G Fresh Da Amaryarsa Sadiya Haruna Ya Shiga Tangal-Tangal Cikin Kasa Da Mako Uku Da Yi



Da alamu dai an fara dauki ba dadi tsakanin ma'auratan nan da sukayi fice a Tiktok, Sadiya Haruna da Angonta Al-Ameeb G. Fresh (Kano material), inda wani faifan bidiyo da angon nata ke bayyana damuwarsa akan auren nasu da ko wata 3 bai cika ba.


Ya ce "Kowa yasan ni bana kazafi, bana karya, soyayya ce ta ja ni, idan ma ance mani wawa ba komi nasan soyayyar ta ce ta ja ni to amma idan na fito nace zan fadi me matata (Sadiya Haruna) tayi mini akan wannan auren namu zaku sha mamaki, zaku tsaneta shekara 10". 


Sai dai wata majiya ta ruwaito G. Fresh yace saki bai shiga tsakanisu ba "har yanzu igiyar aurenta uku suna nan"


"Allah ya shiryeta idan mai shiruwa ce," inji Al-Ameen G. Fresh. Me za ku ce kan wannan al'amari mai cike da mamaki? 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post