Rundunar sojin Najeriya sun damke wata Soja a Najeriya bisa laifin yin aure yayin da take bakin aiki.
Ana zarginta da karya dokar soji ta hanyar nuna soyayya a lokacin da take sanye da kayan aiki. Hotunan bidiyo sun nuna ta na karbar zobe daga wani mutum da ya durkusa a gabanta.
Wata kungiyar kare hakkin mata ta ce sojoji ba su yi mata adalci ba. Sun ce ba a hukunta sojoji maza da suka aikata makamancin haka. Wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya kira matakin da sojojin suka dauka a matsayin "abin kyama".